Siyasa

Kotu Ta Sanya Lokacin Sauraron Ƙarar Da Ganduje Ya Shigar, Kan Batun Dakatar Da Shi

Mai Shari’a, Abdullahi Muhammad Liman, na Babbar Kotun Jihar Kano, ya sanya ranar 28 ga watan Mayun da mu ke ciki, a matsayin ranar da Kotun za ta fara sauraron ƙarar shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya shigar a gabanta, ya na ƙalubalantar matakin dakatar da shi.

Ganduje, na ƙalubalantar matakin dakatar da shi da wasu shuwagabannin jam’iyyar a mazaɓarsa, ƙarƙashin jagorancin Basiru Nuhu Isa, su ka yi ne dai, daga jam’iyyar.

Tun da farko, shuwagabannin mazaɓar ƙarƙashin jagorancin Haladu Gwanjo ne su ka fara dakatar da shi, a ranar 15 ga watan Afrilun da ya gabata.

Daga bisani kuma, wani tsagi na shuwagabannin ya sake dakatar da shi, a ranar 20 ga watan na Afrilun da ya gabata.

Sai dai, Sakataren Jam’iyyar na jihar Kano, Zakari Sarina, ya ce mutanen da su ka dakatar da Gandujen, ba halastattun ƴan jam’iyyar APC bane.

Ganduje kuma, na ƙalubalantar ɗaukar matakin dakatar da shi daga jam’iyyar ne, ba tare da bashi damar kare kansa, kan zarge-zargen da ake masa ba.

Ka zalika, ya na buƙatar Kotun ta ayyana dakatar da shi ɗin da aka yi, a matsayin wanda ba ya kan doka, kuma ta soke matakin.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button