Kotu

Kotu Ta Umarci A Liƙawa Rarara Sammaci A Dukkannin Gidajen Sa

Babbar Kotun Majistiri, mai lamba 1, da ke Lafia, a jihar Nasarawa, ta umarci a liƙawa Fitaccen Mawaƙin siyasar nan, Dauda Adamu Kahutu Rarara, takardar sammacin kiran Kotun, a dukkannin gidajensa, da ke faɗin Najeriya.

Kotun ta bada wannan umarni ne, sakamakon gaza samunsa fuska-fuska domin miƙa masa takardar sammacin da Kotun ta aike masa, kan ƙarar da Fitaccen Ɗan Jaridar nan (Mamallakin Jaridar Rariya Online), Alhaji Sani Ahmad Zangina, ya shigar da shi a gabanta, ya na neman Kotun ta sanya a tsare shi, bisa wasu kalamai da ya furta da Alhaji Sani Zanginan ke musu kallon kalaman tunzuri.

Lauyan mai ƙara, Barista M.A Barde, shi ne ya tabbatar da wannan umarni da Kotun ta bayar, ya yin da ya ke zantawa da Manema Labarai, jim kaɗan bayan fitowa daga zaman Kotun, a yau (Litinin).

Kotun ta kuma sanya, ranar 4 ga watan gobe na Disamba, a matsayin ranar komawa Kotun, domin cigaba da sauraron shari’ar.

Sai dai, a wata tattaunawar wayar tarho da Jaridar ATP Hausa ta yi da Mawaƙin, Dauda Adamu Kahutu Rarara, ya bayyana cewar, takardar Kotu bata riske shi ba. Amma zai sanar da Lauyansa, domin ya bincika.

Idan za a iya tunawa, Mawaƙi Rarara, ya furta wasu kalamai da ake ganin cin zarafi ne, ga muhibbar tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, a ya yin wani taron Manema Labarai da ya gudanar, a jihar Kano, tun a ranar 27 ga watan Oktoban da ya gabata. Inda me ƙara (Sani Ahmad Zangina) ya kasance daga jerin mutanen da ke kallon kalaman na Rarara a matsayin kalaman tunzura al’umma.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button