Kotu Ta Umarci A Tsare Tsohon Gwamnan CBN A Gidan Gyaran Hali
Mai Shari’a Hamza Muazu, na Babbar Kotun Babban Birnin Tarayya Abuja, ya bada umarnin tsare tsohon Gwamnan Babban Bankin Ƙasa (CBN), Godwin Emefiele, a gidan gyaran hali na Kuje, har sai Kotun ta bayyana matsayarta kan buƙatar bayar da shi beli.
Emefiele zai cigaba da zama tsare a gidan gyaran halin ne, har ya zuwa ranar 22 ga watan Nuwamban da mu ke ciki, inda Kotun za ta bayyana matsayarta kan buƙatar da Lauyansa ya gabatar a gabanta, na neman damƙa shi a hannun beli.
A ya yin zaman Kotun da ya gabata ne, Godwin Emefiele, ta hannun Lauyansa, Mathew Burkaa mai lambar anini ta SAN, ya buƙaci bayar da Emefiele ɗin beli, ya yin da Rotimi Oyedepo, ya yi suka a madadin Gwamnatin tarayya.
Bayan suka kan buƙatar ne kuma, sai Alƙalin Kotun, Mai Shari’a Hamza Muazu, ya sanar da jingine hukunci kan buƙatar, har sai a zaman Kotun na gaba.
Alƙalin ya ce, ya na buƙatar lokaci, domin nazartar bayanan ɓangarorin guda biyu.
Zuwa lokacin da mu ke haɗa muku wannan rahoto kuma, tuni Kotun ta buƙaci shuwagabannin gidan gyaran hali na Kuje, da su kawo Mota, domin tasa ƙeyarsa zuwa Gidan ajiya da gyaran halin.