Kotu Ta Umarci Gwamnatin Tarayya Ta Dai-Daita Farashin Kayayyaki Cikin Kwanaki 7
Babbar Kotun tarayya, da ke Lagos, ta umarci gwamnatin tarayya da ta dai-daita farashin kayayyaki, tare da albarkatun manfetur a ƙasar nan, cikin kwanaki bakwai.
Alƙalin Kotun, Mai Shari’a Lewis-Allagoa, ya umarci Gwamnatin da ta saita Madara, Filawa, Gishiri, Sikari, Ababen Hawa, ɗai-ɗaikun kayayyakin gyare-gyare (spare parts), da makamantansu, har ma da Albarkatun Manfetur, irinsu Diesel, Kalanzir, da makamansu.
Alƙalin, ya zartar da wannan hukunci ne, a ranar Talata, kan shari’a mai lamba FHC/L/CS/869/2023 da fitaccen Lauyan nan, Femi Falana ya shigar a gabanta, inda ya ke ƙarar hukumar kula da farashin kayayyaki, da Atoni Janar na tarayya.
Falanan dai, ya buƙaci Kotun da ta umarci hukumar ta ƙayyade farashi da ta sauke haƙƙin da sashe na 4 na dokar ƙayyade farashin kayayyaki ya ɗora mata, na sauƙaƙa yadda farashin kayayyaki zai kasance.
Bayan sauraron hujjojin da Falanan ya gabatar kuma, Alƙalin Kotun Lewis-Allagoa, sai ya amince da dukkannin buƙatun da Falanan ya gabatar, duba da yadda waɗanda ya ke ƙarar su ka gaza bayyana a gaban Kotun, domin kare kansu.