Kotu Ta Umarci Makarantu Su Bawa Masu Murɗaɗɗen Gashi Damar Karatu, A Malawi
Babbar kotun Malawi ta umarci Maáikatar Ilimin kasar da ta bawa daliban da gashinsu ke da daure-daure damar shiga makarantun gwamnatin kasar.
A ranar Litinin ne dai kotun ta kuma kara da umartar maáikatar Ilimin da ta fitar da bayani kan lamarin nan da ranar 30 ga watan Yuni mai kamawa, ta na mai sanar da cire haramcin da aka dorawa daliban kabilar Rastafari, na halartar makarantun gwamnatin kasar.
Wannan hukuncin kotun kuma, ya zo ne bayan karar da aka shigar gabanta a madadin wasu yan kabilar Rastafari guda biyu, wadanda aka gaza basu guraben karatu a makarantun gwamnatin kasar a shekarun 2010 da 2016, sakamakon cukurkudadden gashin da su ke da shi mai tsawon gaske. Daliban dai, karkashin kungiyoyin kare hakkokin dan Adam su ne su ka shigar da karar wacce ke bukatar bawa yaran kabilar ta Rastafari damar halartar makarantun gwamnati, ba tare da wata tsangwama ba, kamar yadda kafafen yada labaran kasar su ka rawaito. A ya yin da ta ke yanke hukunci, a ranar Litinin, Mai Shariá Nzione Ntaba, ta bukaci maáikatar ilimin kasar da ta fitar da wani jawabi wanda zai bayyana bawa daliban kabilar ta Rastafari da ke da nadadden gashi damar shiga ajujuwa. Inda kuma za a fitar da wannan jawabi zuwa ranar 30 ga watan Yuni.
Kabilar ta Rastafari dai, mabiya addinin Abrahamic , da ya samo asali daga Jamaica ne, wadanda ke da tsarin son rayuwa a tsarin da halittar ubangiji ya yi musu, ciki kuwa har da barin gashinsu a yadda ya ke.
Sai dai masu bin wannan kabila a kasar Malawi sun dauki tsawon lokaci su na fuskantar nuna wariya kan shaánonin ilimi, inda ake bukatar dalibai su yi aski domin kasancewa cikin siffa guda.
Kuma, ko a shekarar 2020 ma sai da wata kotu a kasar Kenya ta zartar da irin wannan hukunci wanda ya dakatar da makarantu daga korar daliban kabilar ta Rastafari.