Kotu Ta Umarci Minista Ta Yi Bayanin Yadda Aka Kashe Sama Da Miliyan 500 Wajen Ciyar Da Ɗalibai, A Lokacin Kullen Corona
Babbar Kotun Tarayya, da ke Abuja, ta umarci Ministar Al’amuran Jinƙai, da kare afkuwar bala’o’i, Dr. Betta Edu, da ta yi bayanin yadda aka kashe kimanin Naira miliyan 535.8 wajen gudanar da shirin ciyar da Ɗalibai, a ya yin kullen zaman gida na COVID-19.
Ta cikin hukuncin da ya zartar, Mai Shari’a Nkeonye Maha, ya ce wata ƙungiya ce ta fara buƙatar Ministar ta damƙa mata bayanin yadda shirin ya kasance, kamar yadda sashe na 25(1) na dokar ƴancin samun bayanai ta FOI, ta shekarar 2011 ya yi tanadi.
Mai Shari’a Maha, ta kuma ce gaza amsa buƙatar ƙungiyar, wacce ta aike ta cikin wata wasiƙa mai ɗauke da kwanan watan 6 ga watan Augustan 2020, ba kuma tare da an yi mata bayanin dalilin da ya sanya hakan ba, laifine da ya yi karantsaye ga sashe na 4(a) da (b) na dokar ta FOI.
Hakan kuma ya sanya Kotun ta umarci Ministar da ta miƙa waɗannan bayanai ga waɗanda su ka buƙata cikin kwanaki 21.
Kamfanin dillancin labarai na ƙasa (NAN) ya rawaito cewa: Gidauniyar kare haƙƙin ɗan Adam ta Trustees Of Kingdom ce ta shigar da ƙarar mai lamba FHC/ABJ/CS/1162/2020 a gaban Kotun, biyo bayan zargar Ministar jinƙai ta wancan lokacin, Hajia Sadiya Umar Farouq, tare da Ma’aikatarta da ta yi, da gaza miƙa mata ƙunshin bayanan.