Kotu Ta Yankewa Matashi Hukuncin Ɗaurin Rai Da Rai, Bayan Samunsa Da Laifin Lalata Da Almajirai
Babbar Kotun Jihar Jigawa, Mai Lamba 6, da ke Birnin Kudu, ƙarƙashin Jagorancin Mai Shari’a, Musa Ubale, ta yankewa wani matashi mai shekaru 25 a duniya, Israfilu Sagiru, da ke ƙauyen Zarena, a yankin ƙaramar hukumar hukumar ta Birnin Kudu, hukuncin ɗaurin rai-da-rai a gidan ajiya da gyaran hali, bayan samunsa da laifin aikata fyaɗe (luwaɗi), wanda ya saɓa da sashe na 3 (1) (e) na dokar tauye haƙƙin ɗan Adam (VAPP), doka mai lamba 2, ta shekarar 2021.
Mai magana da yawun Ma’aikatar shari’a ta jihar, Zainab Baba Santali, ita ce ta bayyana hakan, ta cikin wani taron manema labarai da ta gudanar, a ranar Alhamis.
An dai gurfanar da wanda ake zargin a gaban Kotun ne, tun a ranar 5 ga watan Satumban 2021, bisa tuhume-tuhume guda biyu, na yin luwaɗi da wasu Almajirai guda biyu, masu shekara 11 da 12, bayan da ya yi alƙawarin basu kaya, inda ya yi amfani da damar hakan wajen haike musu ta dubura.
Daga cikin shaidun d aka gabatar kuma, akwai waɗanda su ka shaida aukuwar lamarin Ido da Ido, baya ga bayanan da wanda ake ƙarar shi ma ya bayar, har ma da rahoton ƙwararren Jami’in lafiya game da gwajin da aka gabatar akan Almajiran Maza guda biyu.
Da ya ke zartar da hukunci, Mai Shari’a Ubale, ya ce hujjojin da Ma’aikatar shari’ar jihar ta gabatar sun gamsar da Kotun, sun kuma tabbatar da cewa, wanda ake zargin ya aikata laifinsa, dan haka Kotun ta yanke masa hukuncin ɗaurin rai da rai a gidan gyaran hali.
Bugu da ƙari, Alƙalin ya ce akwai takaici kan yadda masu aikata irin wannan laifi su ke amfani da wani abin buƙata wajen hilatar Yara masu ƙananun shekaru wajen aikata ba dai-dai ba, inda ya yi kira ga Iyaye da su kasance masu kula da yaransu a kowanne hali.
A halin yanzu, wanda aka zartarwa hukuncin kuma, ya na da wa’adin kwanaki 90 (wata uku) domin ɗaukaka ƙara.