Kotu Ta Yi Watsi Da Ƙarar Da El-Zakzaky Ya Shigar Gabanta
Babbar kotun tarayya, da ke Abuja, ta yi watsi da ƙarar da Jagoran ƙungiyar Islamic Movement in Nigeria (IMN), da aka fi sani da ‘Shi’a’, Sheikh Ibrahim El-Zakzaky, da Matarsa Zinatu su ka shigar gabanta, su na buƙatar kotun ta umarci hukumar kula da shige da fice ta ƙasa (Immigration), ta sake samar musu da takardar tafiye-tafiye (International Passports).
Da ta ke yanke hukunci, Mai Shari’a, Obiora Egwuatu, ta ce Ma’auratan sun gaza gabatar wa da kotun gamsashshiyar hujjar da zata nuna mata cewar an ƙwace, ko fasfo ɗin nasu ya lalace, ko kuma hukumar da su ke ƙarar bata da niyyar sake samar musu da takardar tafiye-tafiyen.
A watan Janairun shekarar 2022 ne dai, El-Zakzaky tare da Matarsa, su ka maka hukumar kula da shige da fice ta ƙasa (NIS), tare da babban kwantirolanta, a gaban kotu, a matsayin waɗanda ake ƙara na 1 da na 2, ta hannun Lauyansu, Femi Falana, mai lambar anini ta SAN, bisa zargin hukumar da gaza sake samar musu da takardar lamunin tafiye-tafiye ta fasfo.
Ka zalika, a cikin waɗanda ake ƙarar, akwai hukumar binciken sirri ta NIA, da hukumar tsaron farin kaya (SSS), a matsayin waɗanda ake ƙara na 3 da na 4.
Ƙarar mai lamba, FHC/ABJ/CS/22/2022 dai, ta buƙaci kotun da ta yi amfani da ƙarfin da doka ta bata,wajen tilasta hukumomin su samarwa Mijin da Matarsa Fasfo.
Inda su ka yi iƙirarin cewar, an ƙwace fasfunansu na farko ne, tare da lalata su, a shekarar 2015, ya yin da Jami’an tsaro su ka rushe gidansu.
Inda su ka buƙaci kotun da ta ayyana gaza sake samar musu da fasfo ɗin da NIS ɗin ta yi, a matsayin wanda ya saɓawa doka, duba da cewar su na fafutukar fita waje, domin neman lafiya ne.
Sai dai, Lauyan hukumar ta NIS, Jimoh Adamu, ya musanta wannan zargi, na gaza samarwa da Ma’auratan Fasfo, ya na mai cewar Ofishinsa ya na gudanar da bincike game da lamarin.