Kotun Ƙoli Ta Amince Da Cigaba Da Amfani Da Tsofaffin Kuɗi
Kotun ƙolin Najeriya, ta amince da cigaba da amfani da tsofaffin takardun kuɗi na Naira, har Illa-Masha’Allahu.
Da ta ke zartar da hukunci kan lamarin a ranar Laraba, Kotun mai Alƙalai bakwai ƙarƙashin jagorancin Inyang Okoro, ta ce za a cigaba da amfani dukkannin tsofaffin takardun kuɗi na Naira 200, 500 da 1,000, har sai Gwamnatin tarayya ta ce wani abu game da lamarin, bayan tuntuɓar masu ruwa da tsaki da ta ke cigaba da yi.
Kotun ta kuma yanke wannan hukunci ne, bayan buƙatar da Atoni Janar, kuma Ministan shari’a na ƙasa, Lateef Fagbemi ya shigar gabanta, a madadin Gwamnatin tarayya.
Idan ba a manta ba dai, a ranar 3 ga watan Maris ɗin shekarar da mu ke ciki ne, Kotun ta yi watsi da matakin da Gwamnatin tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari ta ɗauka, na dakatar da yin amfani da tsofaffin takardun kuɗi.
A wancan lokacin kuma, Kotun ta amince da yin amfani da tsofaffin takardun kuɗin ne har y zuwa ranar 31 ga watan Disamba.