Kotun Ƙoli Ta Kammala Sauraron Shari’ar Zaɓen Nasarawa
A yau (Talata) ne, Kotun Ƙolin Najeriya, da ke babban birnin tarayya Abuja, ta kammala sauraron ɗaukaka ƙarar da Ɗan takarar Gwamnan jihar Nasarawa, a tutar jam’iyyar PDP, Emmanuel Ombugadu, ya shigar gabanta, ya na ƙalubalantar hukuncin da Kotun ɗaukaka ƙara ta zartar, wanda ya sake tabbatar da, Abdullahi Sule, na jam’iyyar APC, a matsayin halastaccen Gwamnan jihar.
Mai Shari’a Kudirat Kekere-Eku, wacce ta jagoranci tawagar Alƙalan Kotun biyar wajen sauraron bayanan Lauyoyin dukkannin ɓangarorin shari’ar biyu, ta ce kotun za ta sanya ranar da za ta yanke hukunci kan lamarin, a nan gaba kaɗan.
Ɗan takarar Gwamnan jihar ta Nasarawa, ƙarƙashin inuwar jam’iyyar PDP, Emmanuel Ombugadu ne dai, ya shigar da ƙara a gaban Kotun, ya na ƙalubalantar sakamakon zaɓen da hukumar INEC ta gudanar a watan Maris ɗin 2023, wanda ya bayyana Gwamna, Abdullahi Sule, na jam’iyyar APC, a matsayin halastaccen Gwamnan jihar.
PDP ta hannun Lauyanta, Kanu Agabi, ta buƙaci Kotun da ta jingine hukuncin da Kotun ɗaukaka ƙara ta zartar a ranar 23 ga watan Nuwamban shekarar da ta gabata, wanda ya tabbatar da Abdullahi Sule, a matsayin Gwamnan jihar.
Agabi, ya kuma roƙi Kotun, da ta dawo da hukuncin da Kotun sauraron shari’ar zaɓen Gwamnan jihar ta zartar, a ranar 2 ga watan Oktoba, wanda ya bayyana Ɗantakar PDP, Ombugadu, a matsayin wanda ya lashe zaɓen jihar.
Ya kuma ce Kotun ɗaukaka ƙarar ta yi kuskure wajen soke hukuncin Kotun ta tribunal, wanda ya yi fatali da nasarar Gwamna Abdullahi Sule, na jam’iyyar APC, a zaɓen ranar 18 ga watan Maris ɗin 2023.