Kotun Ɗaukaka Ƙara Ta Caccaki Hukumar INEC
Kotun ɗaukaka ƙara, da ke babban birnin tarayya Abuja, ta caccaki Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC), bisa zarginta da ɗaukar ɓangare.
Da yammacin yau (Juma’a), Kotun tace haƙiƙa hukumar tana tafka abin kunya, duba da yadda take iya tsayawa a gaban Kotun domin kare wata jam’iyya, ko nisanta kanta da wasu takardun da su ka fito daga gareta, duk kuwa da yadda sitamfinta ke ɗauke ɗoɗar a jikin takardun.
Ta kuma ce, hukumar zaɓen na cigaba da “falfala gudu a cikin kasuwa”, duk kuwa da buƙatar da ke akwai na kasancewarta ƴar ba ruwanmu, a matsayinta na hukumar da ke gudanar da zaɓe.
“A matsayin INEC na hukuma ya na da kyau ta san matsayinta a fagen zaɓe; kuma ta kasance bata goyon bayan wani tsagi a cikin jam’iyyu.
“Akwai buƙatar ta dakatar da gudanar da wasu ɗabi’un, domin zaman ƙasar nan lafiya.
“Hurumin INEC (idan an zo gaban Kotu) shi ne ta tabbatar da sahihancin kayayyakin da ta san an yi amfani da su lokacin zaɓe, da abin da aka yi da su, har ma da yadda aka samo su.
“Ya kamata INEC ta daina rawa a idon kasuwa, tana ganin kamar babu wanda ya ke lura da abin da take yi”, a cewar Kotun, ya yin da take zartar da hukunci kan shari’ar zaɓen Majalissar jihar Bauchi da aka ɗaukaka.
Kotun mai Alƙalai uku, ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a, K.I. Amadi ta soke nasarar da shugaban Majalissar Dokokin jihar ta Bauchi, Abubakar Suleiman ya samu, a matsayin Ɗan Majalissa mai wakiltar Ningi ta tsakiya, tare da damƙata ga Abokin burminsa na siyasa.