Kotun Ɗaukaka Ƙara Ta Sanya Ranar Fara Sauraron Shari’ar Zaɓen Gwamnan Kano
Kotun ɗaukaka ƙara, da ke babban birnin tarayya Abuja, ta sanya ranar Litinin, 6 ga watan Nuwamban da mu ke ciki, a matsayin ranar da za ta fara sauraron ƙarar da Abba Kabir Yusuf ya ɗaukaka, ya na ƙalubalantar nasarar da Kotun sauraron shari’ar zaɓen Gwamnan jihar Kano, ta bawa, Nasiru Yusuf Gawuna, na jam’iyyar APC.
Sanarwar da Kotun ta fitar, ta bayyana cewar, za a fara sauraron shari’ar mai lamba: CA/KN/EP/GOV/KAN/34/2023 ne, a waccar ranar da aka ayyana.
Waɗanda ke a matsayin masu ƙara a shari’ar sun haɗarda: Gwamna Abba Kabir Yusuf da Jam’iyyarsa ta NNPP, ya yin da jam’iyyar APC da Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta Ta Ƙasa (INEC) su ke a matsayin waɗanda ake ƙara.
Idan za a iya tunawa dai, tun a ranar 20 ga watan Satumban shekarar da mu ke ciki ne, Kotun sauraron shari’ar zaɓen Gwamnan jihar Kano ta sako nasarar Gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf, na jam’iyyar NNPP, bayan da ta yi fatali da 165,663 daga cikin ƙuri’un da aka kaɗa masa, bayan da ta tabbatar da rashin sahihancinsu, sakamakon rashin sa hannun Jami’an hukumar INEC, da Sitamfin hukumar, inda ta miƙa nasara ga, Nasiru Yusuf Gawuna, na jam’iyyar APC, wanda ya kasance na biyu a zaɓen.
INEC, ta ayyana Abba Kabir Yusuf, a matsayin wanda ya samu nasara a zaɓen ranar 18 ga watan Maris ɗin shekarar da mu ke ciki ne, bayan da ya samu ƙuri’u 1,019,602, inda ya doke Abokin karawarsa na APC, Nasiru Yusuf Gawuna, wanda ke da ƙuri’u 890,705.
Sai dai, bayan da Kotun sauraron ƙarar zaɓen Gwamnan Kanon ta cire ƙuri’u, 165,663 daga cikin jimillar ƙuri’un da Abba Kabir Yusuf ɗin ya samu, sai jimillar ƙuri’unsa su ka ragu zuwa 853,939, inda Nasiru Yusuf Gawuna, na APC ya koma samansa da sama da ƙuri’u 30,000, idan aka yi duba da 890,705 ɗin da ya rabauta da su.
Hakan ne kuma ya sanya, Kotun ta ayyana ɗan takarar na APC, Nasiru Yusuf Gawuna, a matsayin wanda ya samu nasara, tare da umartar hukumar zaɓe ta INEC da ta karɓe shaidar samun nasarar da ta bawa, Abba Kabir Yusuf, tare da miƙa sabo ga Nasiru Gawuna.
Sai dai, Abba Kabir Yusuf, da Jam’iyyarsa ta NNPP, tare da hukumar INEC sun ƙi amincewa da sahihancin wannan hukunci, inda su ka ɗaukaka ƙara.