Siyasa

Kotun Ɗaukaka Ƙara Ta Sanya Ranar Yanke Hukuncin Zaɓen Gwamnan Kano

Kotun Ɗaukaka Ƙara, da ke babban birnin tarayya Abuja, ta sanya ranar Juma’a, 17 ga watan Nuwamban da mu ke ciki (gobe), a matsayin ranar da za ta zartar da hukunci kan shari’ar da jam’iyyar NNPP tare da ɗan takararta na zaɓen Gwamna, kuma Gwamnan Kano a yanzu, Abba Kabir Yusuf, su ka shigar gabanta, su na neman Kotun da ta jingine hukuncin da ƙaramar Kotun sauraron shari’ar zaɓen Gwamnan jihar ta yanke, wanda ya bawa ɗan takarar jam’iyyar APC, Nasiru Yusuf Gawuna nasara.

Kotun ta farko dai, ta zartar da hukuncin da ya bawa ɗan takarar APC ɗin nasara ne, bayan da ta zaftare sama da ƙuri’u 165,000 daga cikin ƙuri’un da ɗan takarar NNPP ya samu, bisa hujjar rashin kwanan wata da sanya hannun Jami’an hukumar INEC a jikin takardun.

Kotun ɗaukaka ƙarar kuma, ta sanar da ranar yanke hukuncin ne, ta cikin wasu takardun sanarwa da ta aikewa jam’iyyun NNPP da APC, tare da hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC), kwanaki 10, bayan sauraron shari’ar.

Sanarwar ta bayyana cewar, za a yanke hukuncin ne a gobe (Juma’a) da misalin ƙarfe 9:00 na safiya.

Shari’ar ta Kano kuma, na daga cikin shari’un zaɓe mafiya jan hankali, duba da yadda kujerar Gwamnan jihar ta kuɓuce daga hannun jam’iyya mai mulki ta APC.

Lokaci, shi ne zai tantance yadda hukuncin na gobe ka iya kasancewa.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button