Siyasa

Kotun Ɗaukaka Ƙara Ta Sutale Gwamnan Zamfara, Bayan Da Ta Ayyana Zaɓen Jihar A Matsayin Wanda Bai Kammala Ba

Kotun ɗaukaka ƙara, da ke babban birnin tarayya Abuja, ta soke nasarar da Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal ya samu, a zaɓen 2023 da ya gabata.

A ranar 18 ga watan Maris ɗin shekarar da mu ke ciki ne dai, hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa, INEC ta ayyana, Dauda Lawal na jam’iyyar PDP, a matsayin wanda ya lashe zaɓen Gwamnan jihar.

Sai dai, jam’iyyar APC ta ƙalubalanci nasarar ta, Dauda Lawal na jam’iyyar PDP, inda ta garzaya Kotu, domin neman soke nasarar tasa.

Sai dai, Kotun sauraron ƙarar zaɓen Gwamnan jihar, a karon farko, ta sake ayyana, Dauda Lawal ɗin a matsayin wanda ya lashe zaɓen, lamarin da ya sanya jam’iyyar APC garzayawa gaban Kotun ɗaukaka ƙara.

A yau (Alhamis) ne kuma, Kotun ɗaukaka ƙarar mai Alƙalai uku, ta yi watsi da hukuncin da kotun farko ta yanke, wanda ya bawa Dauda Lawal na PDP nasara, tare da umartar a sake gudanar da zaɓe a wasu ƙananan hukumomi uku na jihar, domin sanin wanda ya yi nasara.

Ƙananan hukumomin da lamarin ya shafa, sun haɗar da: Maradun, Birnin Magaji, da ma ƙaramar hukumar Bukuyun.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button