Addini

Kuɗin Kujerar Aikin Hajjin Bana Ba Zai Haura Miliyan 4.5 Ba – NAHCON

Ta cikin wani jawabi da ta fitar, ranar Juma’a, hukumar Aikin Hajji Ta Ƙasa (NAHCON), ta ce tana kyautata zaton kuɗin Kujerar Aikin Hajjin Maniyyatan Najeriya, ba zai haura Naira miliyan Huɗu Da Rabi, kamar yadda aka ce su miƙa ba, sakamakon irin ƙoƙarin da shugaban riƙo na hukumar, Jalal Ahmad Arabi ya ke yi, ba dare ba rana, tare da tawagarsa.

Jawabin mai ɗauke da sa hannun Mataimakiyar Daraktan yaɗa labarai na hukumar, Fatima Sanda Usara, ya ce “Muna kyautata zaton kuɗin kujerar Aikin Hajji ba za ta haura Naira 4,500,000 ba, kamar yadda aka buƙaci hakan a matsayin mafi ƙanƙantar abin da ma’aikata za su ajiye, a halin yanzu, domin nuna sha’awar halartar Aikin Hajjin 2024.

Amma fa lamarin ya so ya zarce hakan, kawai ƙoƙarin shugaban NAHCON da tawagarsa ne ya sanya mu ke ganin kuɗin ba za su shallake abinda mu ka faɗa ba”.

Usara, ta kuma bayyana cewar, yunƙurin ƙarin da aka samu, ba ya rasa nasaba da halin matsin tattalin arziƙin da ake fuskanta, a ƙasar nan.

Ta kuma ce, an tattauna da shugaban hukumar kan wannan lamari, ta cikin shirin ‘Gane Mani Hanya’ na kafar yaɗa labarai ta BBC Hausa, wanda kuma za a sanya a gobe.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button