Ku Daina Cin Naman Da Aka Ƙunshe A Jarida – Gargaɗin Masana
Ba baƙon abu bane, yadda ake ƙunshe dukkannin wani nau’in nama da aka saya a Najeriya cikin Jarida, ko wasu takardu da ake ganin wa’adin aikinsu ya kai ƙarshe, sai dai masana lafiya sun ga baiken wannan lamari, tare da bayyana ire-iren illolin da hakan ka iya haifarwa.
Masanan dai, sun yi gargaɗin cewar ƙunshe naman a cikin Jarida ko tsohuwar takarda na iya haifar da ciwon daji (Cancer), ko haddasa ciwon wani ɓangare na jikin ɗan Adam.
A madadin hakan, masana lafiyan sun shawarci masu sayar da abubuwan cin da ke buƙatar ƙunshewa da su dinga sanya shi a takardun aluminium.
Hukumar lafiya ta duniya (WHO) ta bayyana cewar, yawaitar sanya abinci a cikin mazubai marasa tsaftace na iya haifar da illa ga ƙwaƙwalwar ɗan Adam, har ma da barazanar rasa rai.