Ku Dinga Kallon Kanku A Matsayin Wakilan Ubangiji, A Bayan Ƙasa – Kiran Babban Joji Ga Sababbin Alƙalai
Alƙalin Alƙalai na ƙasa, Olukayode Ariwoola, ya bayyanawa sababbin Alƙalan Kotun Ƙoli guda 11 cewar, su wakilan Ubangiji ne a bayan ƙasa.
Ariwoola, ya bayyana hakan ne a ranar Litinin, ya yin rantsar da sababbin Alƙalan Kotun Ƙolin da ya gudana a yau.
Ka zalika, ya buƙace su da su kasance masu kare kima da martabar Kotun ta Ƙoli, tare da gudanar da aiki tuƙuru duba da kasancewar hakan babban jigo a fannin shari’a.
Sababbin Alƙalan da aka rantsar su ne: Mai Shari’a Haruna Tsammani (Arewa Maso Gabas), Mai Shari’a Moore Adumein (Kudu Maso Kudu), Mai Shari’a Jummai Sankey (Arewa Ta Tsakiya), Mai Shari’a Chidiebere Uwa (Kudu Maso Gabas), da Mai Shari’a Chioma Nwosu-Iheme (Kudu Maso Gabas).
Sauran su ne: Mai Shari’a Obande Ogbuinya (Kudu Maso Gabas), Mai Shari’a Stephen Adah (Arewa Ta Tsakiya), Mai Shari’a Habeeb Abiru (Kudu Maso Yamma), Mai Shari’a Jamilu Tukur (Arewa Maso Yamma), Mai Shari’a Abubakar Umar (Arewa Maso Yamma), da Mai Shari’a Mohammed Idris (Arewa Ta Tsakiya).