Tsaro

Ku Kai Rahoton Duk Ɗan Sandan Da Ya Yi Ƴunƙurin Fisge Muku Waya – Saƙon Rundunar Ƴan Sanda

Kakakin rundunar ƴan sanda ta ƙasa, Olumuyiwa Adejobi, ya shawarci al’ummar ƙasar nan da su kai rahoton dukkannin Jami’in Ɗan Sandan da ya tilasta wajen karɓar wayoyinsu na hannu, ko bincikar wayoyin.

Adejobi, ya bayyana wannan buƙata ne, ta shafinsa na kafar sadarwa ta X, a ranar Talata.

Inda ya wallafa, “Ku kai rahoton dukkannin Jami’in Ɗan Sandan da ya tilasta karɓa ko bincikar wayoyinku da sauran kayayyakin da ke amfani da lantarki. Domin hakan bai dace ba, ba kuma ƙwarewa a ciki.

“Za su iya buƙatar wayoyinku ne kawai, idan sha’anin bincike ya biyo ta kai, amma hakan ba zai taɓa yiwuwa akan titi ba.

“Saboda haka, dukkannin Jami’in da ya yi yunƙurin bincikar wayoyinku a bakin titi, bai yi dai-dai ba, kuma ya take umarnin Sufeto Janar na ƙasa, da tanadin SOP. Wajibi ne kuma a hukunta shi.”

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button