Tsaro

KUNGIYOYI MASU ZAMAN KANSU SAMA DA 200 SUNYI ZANGA-ZANGAR LUMANA, TARE DA KIRA GA SHUGABAN KASA DAYA KARRAMA MINISTOCIN TSARO

Daga Hauwa Farouk

Wata kungiya mai suna Association of Concerned Citizens tare da hadin gwiwar kungiyoyi masu zaman kansu sama da 200 sun gudanar da zanga zangar lumana a Abuja inda sukayi kira ga shugaban kasar Nigeria Asiwaju bola ahmed tinubu daya karrama ministocin tsaro His Excellency Muhammad Badaru Abubakar da Dr. Muhammad Bello Matawallen Maradun, saboda gagarumar gudummawar da suka bayar a sha’anin tsaron kasar nan,

Da yake magana da manema labarai Shugaban kungiyar kwamared Ekemini Bassey ya bayyana wasu daga cikin gagaruman nasarorin da ministocin suka samu wadanda suka hadar da, inganta tsaro a yankin Neja Delta wanda hakan ya haifar da karuwar hako mai. Daga ganga 900,000 a kowace rana shekara guda da ta wuce, yanzu mun kai kusan ganga miliyan 1.7 a kowace rana. Wannan haɓakar samarwa shaida ce ga ingantattun matakan da ministocin tsaron suka dauka tare da sojojin kasar nan..

Bugu da kari, kokarin ministocin ya taimaka wajen rage kai hare-hare kan ma’adinan mai, wanda a sanadiyyar hakan an samu karin zaman lafiya da kwanciyar hankali na yankin gaba ɗaya.

Haka zalika, sakataren kungiyar da ya fito daga yankin Arewa Maso Yamma Comr zahradeen Muhammad ya bayyana cewa an tayar da sansanonin yan fashin daji sama da dari a yankin Arewa baki daya, a kasa da wata daya da hawansu, inda yanzu duk yawancin inda matsalar take an saka sojoji suna tsare da wajajen, wanda hakan ya haifar da zaman lafiya da kwanciyar hankali musamman a inda matsalolin tsaro sukafi ta’azaara irinsu Kaduna, Katsina, Zamfara, sokoto, niger, benue da kuma jihar maiduguri..

Lokaci bazai bamu damar bayyana irin gagarumar gudummawar da suka bayar ba amma idan akayi la’akari da wadannan Nasarorin na ban mamaki, sun cancanchi yabo da kuma jinjina, domin kuwa jajircewarsu ba iya zaman lafiya kadai ya kawo ba, ya taimakawa wajen cigaban kasa.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button