Ilimi
Kusan Ɗalibai Miliyan 2 Ne Su Ka Yi Rijista, Ya Yin Da Ake Shirin Rufe Rijistar JAMB A Daren Yau
Ya yin da ake shirin kawo ƙarshen rijistar UTME a daren yau (Litinin), hukumar JAMB ta bayyana cewar, sama da Ɗalibai 1,975,926 ne su ka yi rijista, a tsawon makonnin da aka shafe.
An fara rijistar JAMB ne dai, a ranar 15 ga watan Janairun da ya gabata, ya yin da ake shirin ƙarƙare rijistar a ranar Talata, 27 ga watan Fabrairun da mu ke ciki.
Kimanin Ɗalibai 260,249 ne kuma su ka yi rijistar jarrabawar gwaji ta Mock, wacce ake fatan rubutawa a ranar Alhamis, 7 ga watan Maris.
JAMB, ta buƙaci dukkannin ɗaliban da su ka yi rijistar Mock ɗin kuma da su fara cire Slips ɗin jarrabawarsu, daga gobe Talata, 27 ga watan Maris, domin tozali da rana, lokaci, da ma wuraren da za su rubuta jarrabawoyinsu.