Kwalejin Koyon Aikin Noma Ta Audu Baƙo Ɗambatta Ta Fara Sayar Da Form
Kwalejin Koyon Ayyukan Noma Da Kiwo ta Audu Baƙo, da ke Ɗambatta a jihar Kano, ta fara sayar da Online Admission Form, na kakar karatu ta 2023/2024.
Dukkannin ɗaliban da ke da sha’awar karatu a Kwalejin za su iya cike Form ɗin, a shafin makarantar na, www.abcoad.edu.ng, inda ake sayar da Form ɗin karatun Certificate akan Naira 6,000; sai kuma Form ɗin Diploma da National Diploma da ake sayarwa akan Naira 6,500; da kuma Form ɗin karatun Babbar Diploma ta ƙasa (HND) da makarantar ke sayarwa akan Naira 7,000.
Dukkannin Ɗaliban da ke da sha’awar neman gurbin Karatun Diploma ta ƙasa (ND) a makarantar, Wajibi ne su sanya Kwalejin a matsayin zaɓinsu na farko, a shafin hukumar JAMB, tare da ɗora sakamakonsu na kammala Makarantun Sakandire a shafin.
Ka zalika, su ma Ɗaliban da su ka sanya wasu Makarantun a matsayin zaɓukansu na Farko (First Choices), kuma su ke son sauyawa zuwa Kwalejin ta Audu Baƙo, su na damar yin hakan, ta hanyar halartar JAMB CBT Centre mafi kusa da su.