Kwamishina Ya Yi Barazanar Hallaka Alƙalai Kan Shari’ar Zaɓen Gwamnan Kano
Kwamishinan ƙasa da safayo na jihar Kano, Adamu Aliyu Kibiya, ya buƙaci Alƙalan da za su yanke hukuncin Shari’ar Gwamnan jihar da su zaɓa tsakanin rayukansu da kuɗaɗen da su ka karɓa, bayan da aka yi zargin basu na goro.
Aliyu, ya yi wannan barazana ne dai, a ranar Alhamis, ya yin da ya ke jawabi, a taron zanga-zangar da jam’iyyar NNPP wacce ke mulki a jihar ta shirya, jim kaɗan bayan Idar da Sallar Nafila, tare da yin Addu’o’i.
A jawabin nasa ga membobin jam’iyyar NNPP, Aliyu ya ce, “Dukkannin Alƙalin da ya karɓi cin hanci ya yi hukuncin da ba dai-dai ba, muna son sanar da shi cewar, dole ne ya zaɓa tsakanin rayuwarsa da kuɗin cin hancin da ya karɓa”.
Wani fai-fan bidiyo da ke nuna ya yin da Kwamishinan ya ke furta wannan barazana dai, na cigaba da yaɗuwa a kafafen sada zumunta na zamani.
Wannan lamari kuma, na zuwa ne, ya yin da ake dakon hukuncin Kotun sauraron shari’un zaɓen Gwamna, kan zaɓen Gwamnan jihar na shekarar 2023, wanda ya bawa, Abba Kabir Yusuf, na jam’iyyar NNPP nasara, inda Nasiru Yusuf Gawuna na APC da jam’iyyarsa ke ƙalubalantar nasarar zaɓen, bayan da su ka ce kamata ya yi ayyana shi a matsayin wanda bai kammala ba (Inconclusive).