Kwamitin COPSUN Ya Buƙaci Majalissa Ta Yi Mi’ara Koma Baya, Kan Kuɗaɗen TETFund
Kwamitin Iyayen Jami’o’i mallakin jihohin kasar nan COPSUN, ya kalubalanci matakin Kwamitin Majalissar Wakilai kan Asusun tallafawa manyan makarantu na TETFund, na tsame Jami’o’i mallakin Jihohi, daga jerin wadanda za su amfana da tallafin asusun na shekarar 2024.
Idan mai bibiyar Rariya Online zai iya tunawa dai, a baya-bayan nan ne, Majalissar Wakilan ta bayyana daukar matakin dakatar da kimanin Naira biliyan 683 na kudaden asusun na TETFund da aka ware domin gudanar da ayyuka a shekarar da mu ke ciki ta 2024, inda ta bukaci daukacin Jami’o’in da su gabatar wa da kwamitinta zane-zane, jerin abubuwan da ake bukata, da ma yadda za a gudanar da ayyukan a rubuce.
Sai dai, ta cikin wani jawabin manema labarai mai dauke da sa hannun sakataren kwamitin, Suleiman Mahdi, a madadin shugaba, Kwamitin ya bayyaa rashin jin dadinsa kan bada wannan umarni.
Mahdi, ya ce matakin d kwamitin majalissar ya dauka, ya na nuna shirye-shiryen sanya Jami’o’i a tsarin cin gashin kansu ne, amma kuma ya na zama karantsaye ga tsarin rarraba iko, wanda hakan ka iya haifar da rigingimu, a tsakanin matakai daban-daban na gwamnati.
Jawabin, ya kuma kara da yin kira ga kwamitin majalisar, da ya yi mi’ara koma baya kan wannan mataki, tare da bada damar cigaba da tattaunawa, idan hakan ya zama wajibi.