Labarai

Kwankwaso Da Abba, Sun Jagoranci Addu’ar Neman Sauƙi Kan Matsin Rayuwa, A Kano

Jagoran ɗariƙar Kwankwasiyya, kuma Ɗantakarar shugabancin ƙasa ƙarƙashin inuwar jam’iyyar NNPP, a zaɓen 2023 da ya gabata, Rabi’u Musa Kwankwaso, tare da Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, da ma wasu jiga-jigan Gwamnatin Kano, sun Jagoranci Sallah, da Addu’o’in neman nasara ga Gwamnatinsu, tare da neman sauƙi kan halin matsin rayuwar da Al’umma ke ciki.

 

Ana kuma gudanar da taron Addu’ar ne yanzu haka, a Filin Mahaha Complex Sports, da ke ƙwaryar birnin Kano.

 

A ya yin taron dai, Limanin da ya jagoranci Sallar, ya yi Addu’ar samun nasara a dukkannin kotunan da ake Shari’a da Gwamnatin ta Kano, da ma Jam’iyyar NNPP baki ɗaya, tare da Addu’ar neman sauƙi kan halin matsin rayuwar da Talakawa ke ciki.

 

Idan ba a manta ba dai, a makon da ya gabata ne, Kotun sauraron shari’ar zaɓen Gwamnan Kano, ta kammala sauraron bayanan ƙarshe daga ɓangaren Lauyan Masu Ƙara, INEC, da ma masu Kariya, inda ta bayyana cewar, za ta sanya rana domin yanke hukunci kan ƙarar, wacce ke ƙalubalantar nasarar, Gwamna Abba Kabir Yusuf, da ma sahihancin kasancewarsa memban Jam’iyyar NNPP.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button