Siyasa

Kwankwaso Ya Bayyana Dalilin Rashin Samun Nasarar NNPP, a Zaɓukan Da Su Ka Gabata

Ɗan takarar shugabancin ƙasa, na jam’iyyar NNPP, a zaɓen da ya gabata, Rabiu Musa Kwankwaso, ya ce jam’iyyarsu ta gaza taɓuka abin a zo a gani a manyan zaɓukan da su ka gabata ne, sakamakon gaza gane tambarin jam’iyyar da magoya bayansu ke yi, a jikin takardar kaɗa ƙuri’a (Ballot Paper).

Kwankwaso ya ce, hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC), ta gaza fitar da Logon Jam’iyyar tasu yadda ya magoya baya za su gane shi.

Da ya ke jawabi, a ya yin taron kwamitin zartarwar jam’iyyar, Tsohon Gwamnan na jihar Kano, ya ce yadda INEC ta fitar da tambarin jam’iyyar tasu kaɗai a zaɓukan da su ka gabata ma, ya isa ya sanya a soke zaɓukan.

Inda kuma, ya gargaɗi hukumar da kada ta sake aikata irin wannan kuskuren, a ya yin zaɓukan jihohin Kogi, Bayelsa, da Imo.

Ka zalika, ya cigaba da bayyana ƙwarin gwuiwarsa kan cewar, idan aka yi duba da yadda jam’iyyar ta samu nasara a zaɓukan da su ka gabata, inda ta zo ta huɗu a zaɓen shugaban ƙasa, duk da cewar ko shekara guda ba a kai da ƙyan-ƙyasarta ba, ti tabbas jam’iyyar za ta zama jagorar jam’iyyu, anan gaba.

Ya kuma ce, jam’iyyar ba zata maka INEC a gaban kuliya, saboda abubuwan da su ka faru ba, duk da cewar, da an yi zaɓen yadda ya kamata, nasararta za ta wuce wacce ta samu, a yanzu.

A nasa ɓangaren, Shugaban jam’iyyar, na ƙasa, Farfesa Ahmed Rufai Alkali, roƙon hukumar ta INEC ya yi, da ta yi gyare-gyare kan ayyukanta na cikin gida, kamar kan Jami’anta na jihohi, dan tsaftace tsare-tsaren da ta ke bijiro da su.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button