Kotu

Limamin Masallacin Abuja Na Zargin Sanata Ndume Da Tura Ƴan Daba Su Hallaka shi, Ya Yin Da Ya Ke Huɗuba

A ranar Litinin ne babbar Kotun tarayya da ke Abuja, ta sanya ranar 6 ga watan Satumba, a matsayin ranar yanke hukunci, kan ƙarar tauye haƙƙin da Imam Ibrahim Lawal (Malam Usama) ya shigar gabanta, inda ya ke zargin Sanata Ali Ndume da Mansur Jarkasa, da tura masa ƴan baranda domin su hallaka shi, bayan da ya gabatar da huɗuba, a Masallacin da ke helikwatar Majalissar tarayya ta Apo, a Zone B, na babban birnin tarayya Abuja.

Kafin sanya ranar yanke hukuncin da Alƙalin Kotun, Justice M. Muazu ya yi dai, sai da aka bawa Lauyoyin Sanata, Mansur Jarkasa, da Babban Sifiritandan Rundunar Ƴan Sanda (CSP) Ibeh Chukwudi damar kare kansu game da wannan zargi, a gaban kotun.

Ta cikin ƙunshin ƙarar Limamin dai, Matarsa Shamsiyya, ta yi iƙirarin cewar, tun a ranar 16 ga watan Yunin 2023 ne, Ndume ɗin ya fita daga cikin wancan Masallaci a fusace, jim kaɗan bayan kammala gabatar da Sallarsa, bayan da ya zargi cewar Mijin nata ya gabatar da huɗubarsa ne kaitsaye a kansa.

“Mai ƙarar ya nusantar da mutane ne akan muhimmancin neman Ilimi, da kuma Aiki da shi, dai-dai da koyarwar Addinin Musulunci, da ma Sunnar Ma’aiki (Sallallahu Alaihi Wasallam)”, Inda ta kuma ƙara da cewar, daga bisani Sanatan ya dawo cikin Masallacin, inda ya ke zaginsa, tare da ci masa zarafi.

Ta kuma rantse, kamar yadda aka gani a kundin shari’ar da ke gaban Kotun cewar, a ranar Lahadi 18 ga watan Yuni, Sanata Ndume da Jarkasa, tare da rakiyar wasu mutane, sun sake halartar Masallacin, dai-dai lokacin da babban Limamin ke shirin Jagorantar Sallah da daddare, inda su ka karɓi na’urar maganar Masallacin (Microphone), tare da bayyana masa cewar hukumomin Masallacin sun dakatar da shi, daga cigba da Jagorantar Sallah (Limanci).

“Limamin kuma, ya yi mamakin aukuwar dukkannin lamarin, Inda ya yanke shawarar cigaba da jagorantar Sallolin Masallacin, Amma guda daga cikin Dattijan da ke Sallah a Masallacin, ya shawarce shi da ya bar Masallacin, kuma nan ta ke ya yi hakan”, a cewarta.

Bugu da ƙari, Matar ta bayyana cewar, an shigar da rahoton aukuwar hakan a Ofishin rundunar ƴan sanda da ke Apo, Amma ya yin da Mijin nata ya ke dawowa gida, “kafin ya ankara, Sai wasu ƴan daba, bisa umarnin wanda ake ƙara na farko (Ndume) da Jarkasa, su ka farmake shi, ta hanyar dukansa a ka, wanda ya haifar masa da gagarumin ciwo a kansa.”

Ba ya ga sauran buƙatu, Lauyan Mai ƙarar, Al-bashir Lawal Likko, ya kuma roƙi Kotun da ta “bayyana cin zarafi, tauye haƙƙi, duka, cutarwa, da ma ciwon ƴan dabar su ka ji wa Mai ƙarar, bayan turo su da waɗanda ake ƙara na 1 da na 2 su ka yi, a matsayin tauye haƙƙin kimanta dukkannin wani ɗan ƙasa da kundin tsarin dokoki ya tanada, a sashe na 34 (1) na gyararren daftarin kundin tsarin Mulkin Najeriya, na shekarar 1999”.

Lauyan ya kuma ƙara da bayyana cewar, a ya yin da aka gabatar da rahoton aukuwar lamarin ga Ofishin hukumar ƴan sanda na Apo, Wanda ya gabatar da ƙarar aka kama, bisa iƙirarin tayar da hankalin Jama’a, inda har aka gurfanar da shi, a gaban Kotun Mijistiri.

Sai dai, Lauyan waɗanda ake ƙarar, (Ndume da Jarkasa), Ben Jones Akpan, ya roƙi kotun da ta yi watsi da buƙatar ɓangaren masu ƙara, duba da rashin alƙiblar iƙirarin da su ke yi.

Inda Lauyan ya bayyana wa Kotun cewar, Kwamitin Masallacin ne su ka dakatar da Babban Limamin, bisa zarginsa da rashin ɗa’a, rashin lura da Masallacin yadda ya dace, da ma barin mutanen da basu cancanta ba, su na shiga Masallacin su yi barci, a ciki.

Inda ya ce sam hakan kuma ba abu ne da ya dace ba, musamman ma yadda ake zargin Limanin da bijirewa, tare da cigaba da gudanar da Limancinsa, duk kuwa da matakin da Kwamitin Masallacin ya ɗauka, na dakatar da shi.

Lauyan ya kuma ƙara da cewar, abin mamakin shi ne yadda Limanin ya ke zargin an tura masa ƴan daba, a hanyarsa ta zuwa Masallaci, duk da cewar an dakatar da shi.

“Abin da ya ci karo da sakin layi na 9(a-i) na kundin mai ƙara shi ne, yadda Membobin Kwamitin Masallacin su ka buƙace shi da ya yi biyayya ga takardar dakatarwar da aka miƙa masa, wacce ke buƙatar ya bar Masallacin, cikin gaggawa.

“Duk kuma da buƙatar ya bar Masallacin, tun bayan dakatar da shi, sai da ya sake zuwa Masallacin a ranar 18 ga watan Yunin 2023, ya kuma dage cewar sai ya jagoranci Salloli, amma aka hana shi, Inda aka umarci mataimakinsa ya yi Limancin Sallolin wannan rana, shi kuma aka shawarce shi ya bar Masallacin, Kuma hakan ya yi.

“Bayan aukuwar hakan kuma, sai mai ƙarar ya bar Masallacin, amma cikin mamaki ya gayyato wasu ƴan daba da su ka zo daga Katsina, ɗauke da Wuƙaƙe, da sauran manyan makamai masu haɗari, su ka mamaye farfajiyar Masallacin, tare da cin zarafin masu Ibada, a wannan Masallaci”, a cewar Lauyan.

Akpan, ya kuma ce, dalilin wannan aika-aika da ƴan dabar su ka yi ne, ya sa aka gaggauta sanar da Jami’an ƴan sanda, inda nan da nan su ka shiga cikin lamarin.

“Isowar Jami’an ƴan sanda wurin ne, ya kawo lafawar lamarin, tare da tsayar da zubar da jinin Jama’a”, Akpan ya faɗa, ya na mai roƙon Kotun, da ta yi watsi da ƙunshin ƙarar.

Shi kuwa, a nasa ɓangaren, Mr. O. Osho, da ke zama Lauyan CSP, roƙon kotun ya yi da ta yi watsi da ƙarar, duba da yadda babu komai a cikinta, sai ɓatawa Kotun lokaci.

Inda ya musanta cewar, rundunar ƴan sanda ta zargi mai ƙarar da aikata laifukan ta’addanci.

Bayan kammala sauraron ɓangarorin ne kuma, sai Kotun ta sanya ranar 6 ga watan Satumba, a matsayin ranar yanke hukunci, kan ƙunshin ƙarar.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button