LISDEL Ta Shirya Taron Ƙarawa Juna Sani Kan Hanyoyin Kare Aukuwar Annoba
Cibiyar LISDEL, haɗin guiwa da Cibiyar Bunƙasa Harkokin Lafiya ta duniya GHAI, sun shirya wani taron ƙarawa juna sani na kwana guda, a yunƙurinsu na kare yiwuwar ɓarkewar annoba.
Taron, wanda ake gudanar da shi kashi hudu a shekara, ana gudanar da shi ne bisa manufar sake duba ƙoƙarin da gwamnati ke yi wajen tunkarar sababbin annobar da ke ɓullowa, a fannonin lafiya da tattalin arziƙi, da ma sauran alámuran da su ka shafi tsaro ta fuskar kiwon lafiyar da Maáikatunta, a jihar Kano.
Da ya ke batu kan buƙatar samar da kuɗaɗe, da nufin shiryawa tunkarar annobar, shugaban LISDEL na jihar Kano, Muhammad Shuaib, ya ce manufar samar da taron ita ce ɗaukar matakan bunƙasa samar da kuɗaɗen tunkarar sababbin annobobin da ke ɓullowa ta fannin kiwon lafiya, a jihar Kano.