Ma’aikatan Jihar Taraba, Sun Bijirewa Umarnin Tsunduma Yajin Aiki
Ma’aikata a jihar Taraba, sun fita aiki kamar yadda su ka saba ko yaushe, a wannan rana ta Talata, duk kuwa da kiran da gamayyar ƙungiyoyin ƙwadago na NLC da TUC su ka yi ga membobinsu, na tsunduma Yajin Aikin Sai Baba Ta Gani, daga safiyar yau.
Wakilin kamfanin dillancin labarai na ƙasa (NAN), ya rawaito cewar, ana gudanar da cikakken aiki ba tare da wata tangarɗa ba, a ofisoshin Gwamnatin jihar, da ke Jalingo, inda ɗaukacin Ma’aikata su ka fito Aiki, kamar yadda su ka saba, a kowacce rana.
Wani Ma’aikacin Gwamnati, mai suna, Tanimu Musa, ya bayyanawa NAN cewar, Yajin Aikin na a matsayin kishiya ne, ga cigaban ƙasa.
Ya kuma ce, basu da wani dalili na tsunduma Yajin Aikin, duba da irin ƙoƙarin da Gwamnatin jihar, da ta tarayya su ke cigaba da yi, ya na mai buga misali da tallafin rage raɗaɗin da Gwamnatin tarayya ke bayarwa, da ma ƙarin Albashin da Gwamnatin tarayya ta yi na wucin gadi, ya yin da ita ma Taraban ta ke biyan Naira 30,000 na mafi ƙarancin albashi.
Ana ganin abin da ya sanya ƙungiyoyin na NLC da TUC tsunduma Yajin Aikin dai, ba ya rasa nasaba da irin dukan kawo wuƙar da Jami’an Ƴan Sanda, su ka yi wa shugaban NLC na ƙasa, Joe Ajaero, tun a ranar 1 ga watan Nuwamban da mu ke ciki, a birnin Owerri, na jihar Imo.
Kafin shiga Yajin Aikin kuma, sai da Kotun ɗa’ar Ma’aikata ta umarci ƙungiyoyin na NLC da TUC da su dakata daga shiga Yajin Aikin nasu, wanda su ka tsunduma a yau Talata, 14 ga watan Nuwamba, bayan da Gwamnatin tarayya ta buƙaci hakan, umarnin da ƴan ƙungiyar ƙwadagon su ka bijirewa.