Ma’aikatar Tsaro Za Ta Haɗa Hannu Da Ma’aikatar Cikin Gida, Domin Inganta Tsaron Ƙasa
Ma’aikatar tsaro ta ƙasa, za ta haɗa guiwa da Ma’aikatar cikin gida, domin yaƙar matsalolin tsaro, a cikin ƙasar nan.
Ministan tsaro, Alhaji Muhammad Badaru Abubakar, shi ne ya bayyana hakan, ya yin da ya karɓi baƙuncin Ministan cikin gida, Mr Olubumi Tunji-Ojo, ya yin wata ziyara da ya kai masa, a babban birnin tarayya Abuja.
Bayanin hakan kuma, na ɗauke ne ta cikin wani jawabi da Daraktan Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a na Ma’aikatar, Mr Henshaw Ogubike, ya fitar, a jiya.
Badaru ya ce, Ma’aikatar ta cimma ɗumbin nasarori ta fuskar yaƙi da matsalolin rashin tsaro, kuma a shirye ta ke ta yi Aiki da Takwararta ta cikin gida, domin tsamo ƙasar nan daga matsalolin rashin tsaron da su ka mamayeta.
Ministan, ya buƙaci a kafa kwamiti a tsakanin ma’aikatun guda biyu, da za su yi aikin tunkarar ƙalubalen tsaron na ƙasar nan.
Tun da farko, Tunji-Ojo, ya bayyana cewar akwai buƙatar ma’aikatar ta cikin gida ta ƙarawa kanta ƙarfin yaƙi da matsalolin tsaro, ta hanyar haɗa guiwa da ma’aikatar tsaro.
Ya kuma ce, abubuwan da ake gani a ƙasa zuwa yanzu, sun sha ban-ban da yadda ake gani shekaru 15 da su ka gabata.