Kasuwanci

Magatakardan CITM, Ya Yi Kira Da a Samar Da Dokar Haramta Jibge Kuɗaɗen Ƙetare

Magatakardan Cibiyar Kula da harkokin ajiya ta CITM, Mr Olumide Adedoyin, ya yi kira ga Majalissar taarayya, da ta samar da dokar da za ta haramta jibge kudaden ketare, a fadin kasar nan.

Adetoyin, ya yi wannan kira ne, ya yin da ya ke zantawa da kamfanin dillancin labarai na kasa NAN, yau Laraba, a babban birnin tarayya Abuja, kan yadda darajar Naira ke kara faduwa kowacce rana, idan aka kwatanta da Dalar Amurka.

Ya kuma roki gwamnati, da ta dauki matakan da za su kare martabar kudaden kasarta, ta hanyar samar da dokokin da za su kare darajar Naira.

Da ya ke martani, kan jawabin Gwamnan babban bankin kasa, Mr Olayemi Cardoso, wanda ya ce darajar Naira na komawa baya, Adetoyin ya ce, ana cutar da takardar kudi ta Naira ne, ba wai darajarta ce ke raguwa ba.

Ya kuma ce, akwai bukatar yan siyasa su dauki kwararan matakai, ta fuskar haramta mallakar kudaden ketare ba bisa ka’ida ba, da ma jibge da ake ba tare da yin amfani da shi ba.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button