Magidanci Ya Shafe Mako Guda Ya Na Tattaki, Domin Kai Ziyara Ga Mutumin Da Ya Maka Rarara A Kotu
Wani Magidanci, mai suna, Malam Adamu, ya shafe tsawon kwanaki 7 ya na tattaki a ƙafa, daga garin Argungu na jihar Kebbi, zuwa jihar Nasarawa, domin kaiwa Fitaccen Ɗan Jaridar nan, Alhaji Sani Ahmad Zangina ziyara, da nufin nuna farincikinsa, kan ƙarar da ya maka Mawaƙi Dauda Adamu Kahutu Rarara a gaban Kotu.
Sani Ahmad Zangina, shi ne ya wallafa hoton Magidancin da ya kai masa ziyarar, a shafinsa na kafar sadarwa ta Facebook, da yammacin ranar Talata, tare da yi masa godiya, haɗe da Addu’ar Allah ya bar zumunci.
“Nayi bako daga garin Argungu ta Jahar Kebbi da yayi tattaki a kasa inda ya kwashe kwana 7 a hanya kawai domin nuna farin cikinsa da karar Mawaki a kotu.
“Malam Adamu ina godiya sosai da sosai Allah yabar zumunchi.”, a cewar Sani Ahmad Zangina.
Idan ba a manta ba dai, a jiya Litinin ne, Babbar Kotun Majistiri Mai Lamba 1, da ke Lafia, a jihar Nasarawa, ta fara sauraron shari’ar da Alhaji Sani Ahmad Zangina, ya shigar da Mawaƙi Rarara, bisa zarginsa da furta kalaman tunzura al’umma, a ya yin wani taron Manema Labarai da ya gudanar, a birnin Kano, tun a ranar 27 ga watan Oktoban da ya gabata.
Gaza halartar Rarara Kotun ne kuma, ya sanya Alƙaliyar Kotun ta umarci a liƙewa Mawaƙin takardar sammaci a dukkannin gidajensa da ke faɗin Najeriya, tare da ɗage cigaba da sauraron shari’ar, zuwa ranar 4 ga watan gobe na Disamba.