Labarai

Majalissar Dattijai Ta Amince Da Ƙudurin Samar Da Hukumar Cigaban Arewa Maso Yamma

A ranar Alhamis ne, membobin Majalissar Dattijai, su ka amince da ƙudirin dokar samar da hukumar cigaban yankin Arewa Maso Yamma, wacce za ta yi aikin shawo kan manyan ƙalubalen da su ka addabi jihohin yankin guda bakwai.

Hakan kuma, ya zo ne bayan duba rahoton Kwamitin Ayyuka na musamman na Majalissar.

Ƙudurin dokar, wanda ya tsallake karatu na uku, Mataimakin Shugaban Majalissar, Sanata Barau Jibrin ne ya gabatar da shi, bisa mara bayan ƙarin ƴan majalissu 20, da su ka fito daga Jihohin yankin na Arewa Maso Yamma.

Shugaban Kwamitin, Sanata Shehu Kaka, wanda ke wakiltar Borno ta tsakiya, ya ce an amince da ƙudirin ne domin bunƙasa tattalin arziƙin yankin.

Ya kuma ce samar da hukumar zai kusanto da gwamnatin tarayya ga mazauna yankin na Arewa Maso Yamma.

A nasa jawabin, Sanata Barau Jibrin, ya yabawa ƴan uwansa ƴan majalissu, waɗanda su ka tsaya kai da fata wajen ganin ƙudurin ya kai labari.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button