Kasuwanci

Majalissar Dattijai Ta Buƙaci Gwamnan CBN Ya Gurfana A Gabanta

Majalissar Dattijai, ƙarƙashin kwamitinta na kula da bankuna, inshora, da cibiyoyin kuɗi, ta buƙaci Gwamnan Babban Bankin Ƙasa (CBN), Olayemi Cardoso, da ya bayyana a gabanta, kafin ranar Talatar makon gobe.

Majalissar ta kuma buƙaci bayyanar tasa ne, dan jin ba’asi kan halin taɓarɓarewar da tattalin Arziƙin ƙasar nan ya tsinci kansa, da ma faɗuwar da takardar kuɗi ta Naira ke cigaba da yi, a kasuwar musayen kuɗaɗe.

Shugaban kwamitin, Adetokunbo Abiru, shi ne ya bayyana wannan kiranye, a ya yin zantawarsa da manema labarai, yau Laraba, a babban birnin tarayya Abuja, jim kaɗan bayan kammala zaman sirri na majalissar.

Abiru, ya ce halin da tattalin arziƙin ƙasar nan ya tsinci kansa, musammanma ta fuskar hauhawar farashin kayayyaki, abu ne da ke ci wa ƴan majalissar tuwo a ƙwarya.

Ya na mai cewa, “Mun gudanar da zaman tattaunawa, duba halin da tattalin Arziƙin ƙasar nan, ya tsinci kansa.

“Dukkanninmu muna raye, muna ganin abin da ke faruwa. Babban abin da ya fi damunmu ma shi ne yadda a kowacce rana tattalin arziƙin ƙasar nan ke ƙara ci baya, ga kuma hauhawar farashin kayayyaki.

“Bayan mun tattauna batun, mun yi sammcin Gwamnan CBN dan ya bayyana a gabanmu, ranar Talata, da misalin ƙarfe 3 na yammaci, domin ba mu bahasi kan halin da tattalin arziƙin ƙasar nan, ya tsinci kansa.”.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button