Majalissar Dokokin Jigawa Ta Dakatar Shuwagabannin Ƙananan Hukumomi, Bisa Zargin Fita Ƙasar Waje
Majalissar Dokokin jihar Jigawa, ta dakatar da shuwagabannin ƙananan hukumomin jihar guda uku, bisa zarginsu da fita daga ƙasar nan, ba tare da neman sahalewar Gwamnatin Jiha, ko Majalissar Dokokin ba.
Jerin shuwagabannin da aka dakatar, sun haɗar da: Hon. Rufai Sunusi na ƙaramar hukumar Gumel; Hon. Mubarak Ahmed, na ƙaramar hukumar Birniwa; da Hon. Umar Baffa, na ƙaramar hukumar Ƴankwashi.
Majalissar ta kuma amince da ɗaukar wannan mataki ne, bayan da shugaban Kwamitin Majalissar Kan Al’amuran ƙananan hukumomi, Hon. Aminu Zakari Tsubut, ya gabatar da buƙatar dakatar da su, sakamakon tafiyar da su ka yi, zuwa Ruwand, ba tare da izini ba.
A ya yin gabagatar da ƙudirin, Tsubut ya bayyana cewar, Majalissar ta umarci shuwagabannin ƙananan hukumomin jihar, da su ƙauracewa zuwa ko ina, sakamakon shirye-shiryen gabatar da ƙudurin kasafin kuɗin jihar na shekarar 2024 da Gwamna, Malam Umar Namadi zai yi.
Inda ya bayyana abin da Ciyamomin su ka aikata a matsayin bijirewa umarni, wanda kuma abu ne da ya dace a bincika, tare da gabatar da hukunci akai, dai-dai da yadda doka ta yi tanadi.
Shima ɗan majalissar ƙananan hukumomin Malam Madori, Hon. Usman Abdullahi Tura; da na Guri, Hon. Hamza Guri, sun sake gabatar da ƙudurin, bayan Tsubut.
Inda a nan take kuma, Majalissar ta amince da dakatar da shuwagabannin guda uku, tare da umartar Mataimakansu da su ɗare kan karagar.
Zauren Majalissar ya kuma kafa kwamitin da zai yi bincike kan lamarin, tare da gabatarwa da zauren Majalissar rahoto cikin makonni huɗu, domin sanin matakin da za a ɗauka na gaba.