Majalissar Dokokin Kano, Ta Amince Da Samar Da Hukumar KARARA
Majalisar dokokin jihar Kano, ta amince da ƙudurin dokar samar da hukumar kula da titunan karkara ta jihar Kano (KARARA).
Mataimakin Shugaba, Wanda ya jagoranci zaman majalissar, a madadin Shugabanta, Alhaji Kabiru Hassan Dashi ne ya gabatar da ƙudurin ranar Litinin, a zauren majalisar, inda daga bisani kuma majalissar ta amince da wannan ƙuduri, wanda a yanzu ya ke a matsayin doka.
Hakazalika majalissar ta karɓi wasiƙa daga majalissar zartawar Gwamna mai barin gado, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, wacce ke neman sahalewar majalisar domin naɗa, Dr. Ibrahim Yakasai, a matsayin shugaban Asibitin Koyarwa na Muhammad Abdullahi Wase, wanda a yanzu ke a matsayin Asibitin koyarwa na ɗaliban Jami’ar Jihar ta Yusuf Maitama Sule, da ke birnin Kano.
Bayan duba kan wannan ƙuduri kuma, majalissar ta amince da sake zama a yau, domin tattaunawa kan yiwuwar naɗa, Dr. Ibrahim Yakasan, a matsayin shugaban Asibitin.