Labarai

Majalissar Wakilai Ta Buƙaci Hukumar Kashe Gobara Ta Mayar Da Kuɗaɗen COVID-19

Majalissar Wakilai, ta buƙaci hukumar kashe gobara, da ta mayar da Naira biliyan 1.48 da aka miƙa mata a ya yin annobar COVID-19, cikin kwanaki bakwai.

Shugaban kwamitin kula da kuɗaɗen al’umma na Majalissar, Bamidele Salam, shi ne ya bada wannan wa’adi, ranar Laraba, a babban birnin tarayya Abuja.

Inda ya buƙaci, Jami’in kula da al’amuran kuɗi na hukumar da ya dawo da kuɗaɗen, bayan da kwamitin ya zargi shuwagabannin hukumar da gaza martaba gayyatar da ta yi musu, har karo huɗu, dan jin ba’asi kan yadda hukumar ta kashe kuɗaɗen da aka ware mata, na COVID-19.

Membobin Kwamitin, sun nuna damuwarsu, kan yadda hukumar ta gaza girmama gayyatar da kwamitin ya yi mata, wanda hakan ne ma ya sanya su ɗaukar wannan mataki.

A gefe guda kuma, kwamitin ya bawa hukumar daƙile yaɗuwar cututtuka ta ƙasa (NCDC), Ofishin Akanta Janar, da Ma’aikatar Noma wa’adin bayyana a gaban kwamitin na ƙarshe, dan jin ba’asin yadda su ka kashe nasu kuɗaɗen, na COVID-19.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button