Ilimi

Majalissar Wakilai Ta Buƙaci JAMB Ta Tsawaita Wa’adin Rijistar UTME

Ƴan Majalissar Wakilai ta tarayya, sun buƙaci hukumar shirya jarrabawar neman shiga manyan makarantu ta ƙasa (JAMB), da ta tsawaita wa’adin rijistar jarrabawar UTME, ta shekarar 2024 da mu ke ciki, da makonni biyu.

Buƙatar hakan kuma, ta biyo bayan ƙudirin gaggawar da Ɗan Majalissa, Hassan Shinkafi na jam’iyyar PDP, daga jihar Zamfara ya gabatar, a ya yin zaman majalissar na ranar Alhamis.

An kuma yi wa ƙudirin ta ke da: “Buƙatar Tsawaita Wa’adin Rijistar JAMB”.

Da ya ke gabatar da ƙudirin, Shinkafi ya ce, an buɗe rijistar UTME ɗin ne, a ranar 15 ga watan Janairun da ya gabata, ya yin da aka rufe rijista, a ranar 26 ga watan Fabrairu.

Ya na mai ƙarawa da cewar, saboda halin matsin tattalin arziƙin da ake fama da shi a ƙasar nan, “Mutane da dama basu samu sukunin yin rijista a wannan wa’adin ba”.

Shinkafi, ya kuma ce matuƙar JAMB bata tsawaita wa’adin ba, to ɗalibai da dama ba za su samu damar yin rijista, da shiga a fafata da su a tsarin neman gurbin karatu na shekarar nan ba.

Da su ke amincewa da ƙudirin, Ƴan Majalissar sun buƙaci JAMB da ta ƙara sati biyu, tare da damƙa aikin tabbatar da hakan ga Kwamitin Ilimi na Majalissar.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button