Majalissar Wakilai Ta Sanya Lokacin Ƙaddamar Da Sabon Kundin Dokokin Ƙasa
Kwamitin Majalissar Wakilai, kan sabunta kundin dokokin ƙasar nan, ya bayyana watan Disamban 2025, a matsayin lokacin da za a ƙaddamar da sabon kundin dokokin ƙasar nan, da aka yi wa kwaskwarima.
Mataimakin shugaban Majalissar Wakilai, kuma shugaban kwamitin, Hon. Benjamin Okezie Kalu, shi ne ya bayyana hakan, ranar Laraba, jim kaɗan bayan zaman da kwamitin ya gudanar, a babban birnin tarayya Abuja.
Kalu, ya ce Kwamitin zai kuma sanya tartibin lokacin da zai ƙaddamar da sabon kundin dokokin ƙasar, cikin watan na Disamban 2025.
Ya kuma ce, wannan shi ne karo na shida, da majalissar ke sabunta daftarin kundin dokokin ƙasar.
Ka zalika, ya ce majalissar za ta yi duba da tarin ƙalubalen da ake fuskanta ta fuskar rashin tsaro, da matsin tattalin arziƙi, ya na mai cewar rabon da a yi wa kundin tsarin mulkin ƙasar kwaskwarima, tun shekarar 2010, bayan gadarsa da aka yi daga hannun sojoji, a shekarar 1999.
Daga cikin gyare-gyaren da ake fatan yi wa kundin dokokin, akwai fannin shari’a, zaɓe, da ma wasu daga cikin al’amuran Gwamnati.
Ya kuma ce, za a ƙaddamar da kwamitin ne, a ranar 26 ga watan Fabrairu, mai kamawa.