Labarai

Majalissar Wakilai Ta Umarci A Kamo Gwamnan CBN, Da Akanta Janar Na Tarayya

Kwamitin Majalissar Wakilai ta ƙasa, kan ƙorafe-ƙorafen al’umma, ya bada umarnin kama Gwamnan Babban Bankin ƙasa, Olayemi Cardoso, Akanta Janar ta tarayya, Oluwatoyin Madein, tare da ƙarin wasu mutane 17, bayan da su ka gaza bayyana a gaban zauren Majalissar domin, amsa wasu tambayoyi, da ke da alaƙa da ma’aikatunsu.

Hakan kuma ya zo ne, bayan ƙudurin da Ɗan Majalissa, Fred Agbedi, na jam’iyyar PDP daga jihar Bayelsa, ya gabatar a ya yin zaman Kwamitin na ranar Talata.

Agbedi dai, ya ce umarnin kama mutanen wajibi ne, duba da yadda su ka ƙauracewa halartar gaban Kwamitin domin amsa tambayoyi.

Ya kuma Majalissar na yin aiki ne, kan doron lokaci, kuma an gayyaci mutanen har karo huɗu, amma basu amsa gayyatar ba.

A yanzu dai, Sufeto Janar na ƙasa ne ke da hurumin taso ƙeyar shuwagabannin, tare da gabatar da su a gaban Kwamitin.

Shugaban kwamitin, Michael Irom, na jam’iyyar APC daga jihar Cross River, ya buƙaci sufeton ƴan sandan ya gabatar da mutanen a gaban majalissa, a ranar 14 ga watan Disamban da mu ke ciki.

Wanda ya shigar da ƙorafi akansu dai, ya ce ƙorafinsa na da alaƙa da tsarin NEITI, da aka gudanar, tun a shekarar 2021.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button