Majalissar Wakilai Za Ta Fallasa Bayanan Masu Hannu A Satar Ɗanyen Mai
Kwamitin da Majalissar Wakilai ta kafa, domin bincike kan sha’anin satar ɗanyen man ƙasar nan, da ma samun raguwar kuɗaɗen shiga da ƙasar ke fama da shi a fannin iskar gas, ya sha alwashin fallasa bayanan waɗanda ke da hannu dumu-dumu a satar man ƙasar nan.
Shugaban Kwamitin, Kabiru Alhassan Rurum, shi ne ya yi wannan barazana, a ya yin zantawarsa da kamfanin dillancin labarai na ƙasa (NAN), gabanin zaman jin ƙwaƙwaƙwafi da kwamitin zai yi a ranar 7 ga watan Satumba.
Inda ya ce, har yanzu dai, fannin na iskar gas shi ne fage ɗaya tilo da ke cigaba da zama jagora ta fuskar samar wa da ƙasar nan kuɗaɗen shiga, ya na mai bada ƙwarin gwuiwar cewar, binciken kwamitin a yanzu, ba zai kasance kamar na baya ba.
Ba ya ga amanna da fetur da iskar gas a matsayin manyan hanyoyin samun kuɗin shigar ƙasar nan da Rurum ɗin ya yi, Ɗan Majalissar ya ce, yawaitar sace-sace ne babban ƙalubalen da fannin ya ke fuskanta, a kowacce rana, kuma cikin kowacce daƙiƙa.
“Dalilin samar da wannan kwamiti shi ne gano su waye kanwa uwar gami, kuma me ma ya ke faruwà a wannan fage na satar ɗanyen Mai”.
Ya na mai cewar, cigaba da ɗora alhakin hakan akan Jami’an tsaro kaɗai ba zai wadatar, ko samar da mafita ba, domin wajibi ne dukkannin masu ruwa da tsaki a fannin, kamar Chevron, Shell, da ma al’umma su haɗa hannu wajen shawo kan wannan matsala, da ke cigaba da zama wutar daji.
“Muna buƙatar sanin asalin masu rura wutar matsalar, saboda bincike, Dan haka akwai buƙatar kowa, ciki har da masu ruwa da tsaki, su zo su labarta mana abin da su ka sani a fagagensu.”
Ya kuma ce tuni kwamitin nasu ya gayyaci rundunar Sojin ruwa, da Sojin Sama, da ma rundunar Civil Defence, Ƴan Sanda, da makamantansu, domin ji daga nasu ɓangarorin.
Ya na mai cewar, za kuma a tattauna yadda za a shawo kan matsalar da fannin ke fuskanta.