Makki Abubakar, Ya Bayyana Sha’awar Shugabantar Majalissa Ta 10
Shi ma ɗan majalissar tarayya, Makki Abubakar Yalleman, ya bayyana sha’awarsa ta shiga a dama da shi, a neman shugabancin majalissar wakilai ta 10.
Yalleman dai, na wakiltar Mallam Madori da Kaugama, da ke jihar Jigawa ne, a majalissar dokokin ƙasa, inda kuma ya ke a matsayin mataimakin shugaban kwamitin tsaro, na majalissar.
Ɗan majalissar, ya kuma bayyana cewar, tsarin karɓa-karɓa da jam’iyyar APC ke da shi, a fagen shugabanci, shi ne ke alamta daga shiyyar da Shuwagaban Majalissar Dattijai, da na wakilai zai fito, kasancewar jam’iyyar ce ke da mafi akasarin kujeru a majalissar.
Ya kuma roƙi jam’iyyar APC, da ta bayar da kujerar shugabancin majalissar ga yankin Arewa, ya na mai cewar, hakan ne zai tabbatar da adalci, a fagen raba kujerun siyasa, a ƙasar nan.
Sai dai, Yalleman ya ce, babu tsarin karɓa-karɓar shugabancin ga shiyyoyi, a kundin tsarin mulkin ƙasa, na 1999, amma hakan, na daga cikin tsarin gwamnatin tarayya.