Malaman Firamare Sun Tsunduma Yajin Aiki A Abuja
Da safiyar yau (Litinin) ne, ƙungiyar Malamai ta ƙasa (NUT), reshen babban birnin tarayya Abuja, ta tsunduma Yajin Aiki.
Ta cikin wata sanarwa, da ƙungiyar ta fitar, a ranar Juma’ar da ta gabata dai, ta umarci ɗaukacin membobinta, da ke yankuna shida na birnin, da su tsunduma Yajin Aiki a yau, sakamakon gazawar shugaban hukumar Ilimin birnin, na gaza biyan Malaman mafi ƙarancin albashi, har tsawon watanni 25, baya ga gaza biyan kuɗaɗen ariyas, da ma kaso 40 na alawus ɗin membobinsu.
Babban Sakataren ƙungiyar ta NUT reshen Abuja, Kwamared Margaret I. Jethro, ya bayyana cewar, Malaman za su fara gudanar da Yajin Aikin ne daga yau, 15 ga watan Janairu, kamar yadda su ka ƙudirta.
Ko a safiyar yau ma kuma, Margaret ɗin, ya bayyanawa Jaridar Daily Trust cewar, duk da wannan barazana ta su ta tsunduma Yajin Aiki, har yanzu shugaban hukumar Ilimin na cigaba da kawar da kai game da batun, ya na mai ƙarawa da cewar, ba a biyan Malaman Albashi tun watan Disamban 2023 da ta gabata, face Malaman da ke shiyyar Abaji kaɗai.
Ko da Manema Labarai, su ka yi yunƙurin tuntuɓar, shugaban ƙungiyar shuwagabannin ƙananan hukumomi na babban birnin tarayya Abuja, Danladi Chiya ta wayar tarho kuma, ya gaza amsa kira, tare da gajeren saƙon da aka aike masa.