Malaman Firamaren Abuja Sun Koma Bakin Aiki, Bayan Tsoma Bakin Wike
Malaman makarantun firamaren babban birnin tarayya Abuja, sun koma Aiki a ranar Litinin, bayan Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyeson Wike, ya sanya baki.
Malaman dai, sun tsunduma Yajin Aikin ‘sai baba ta gani’ ne, da nufin tilasta biya musu buƙatunsu, da su ka haɗarda, biyan kaso 40 na kudaden alawus-alawus, da ma biyan ariyas ɗin mafi ƙarancin albashinsu na tsawon watanni 25, da makamantan waɗannan buƙatu.
Sakatariyar ƙungiyar Malamai ta NUT, reshen babban birnin tarayya Abuja, Margaret Jethro ce, ta bayyana hakan, ya yin zantawarta da kamfanin dillancin labarai na ƙasa, a ranar Litinin.
An kuma kawo ƙarshen Yajin Aikin ne, a yau (Litinin), bayan tsoma bakin Ministan babban birnin tarayya Abuja, cikin lamarin, kan batun biyan kuɗaɗen ariyas na mafi ƙarancin albashin da Malaman ke bin gwamnati.
Sakatariyar, ta ce Ministan ya kuma yi alƙawarin biyansu kaso 40 na kuɗaɗen da su ke bi, sama da biliyan 7, ya yin da hukumar da ke kula da yankin za ta biya kaso 60.
Ta kuma ce, za a fara biyan kuɗaɗen ne, daga watan Janairun da mu ke ciki, ya yin da za a kammala a watan Maris.
Malaman dai, sun tsunduma Yajin Aikin na ‘sai baba ta gani’ ne, a ranar 15 ga watan Janairun da mu ke ciki.