Labarai

Manyan Ma’aikatan Gwamnati Sun Yi Watsi Da Buƙatar Rage Kwanakin Aiki, Saboda Cire Tallafin Mai

Ƙungiyar Manyan Ma’aikatan Gwamnatin Najeriya (ASCSN), ta bayyana cewar, rage yawan kwanakin Aiki ga Ma’aikatan ƙasar nan ya na da illa ta zahiri ga tattalin Arziƙin ƙasa.

Shugaban ƙungiyar na ƙasa, Tommy Okon, shi ne ya bayyana hakan, a ya yin zantawarsa da kamfanin dillancin labarai na ƙasa, ranar Lahadi, a babban birnin tarayya Abuja.

Okon, ya kuma ce, hakan zai haifar da gagarumar illa ta fuskar gudanarwar Aiki.

Idan za a iya tunawa dai, a ranar 29 ga watan Mayu ne, Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya sanar da janye tallafin manfetur, wanda hakan ya haifar da gagarumin ƙalubale ga jama’ar Najeriya da dama ta fuskar tattalin Arziƙi.

Hakan ne kuma, ya tilasta wasu daga cikin Ma’aikata rage Adadin kwanakin aikinsu.

A cewar Okon ɗin kuma, Sam Najeriya ba ta dace da irin wannan tsarin, da mutane za su zauna daga gida su yi Aiki ba.

“Rashin wadatacciyar wutar lantarki, ko kayayyakin Sadarwar Intanet, su ne Manyan ƙalubalen da wannan tsari zai ci karo da su”, a cewar Mr Okon.

Shugaban, ya kuma ƙara da cewar, tsare-tsaren rage raɗaɗin da Gwamnatin tarayya ta ke bijirowa da su, ba su zo akan lokaci ba (an makara).

Inda ya ce, har yanzu Albashin Ma’aikata ya na nan a yadda yake, duk da ire-iren ƙalubalen cire tallafin man da ake fuskanta, wanda ya shafi rayuwar mafi yawan Jama’ar Najeriya.

Bugu da ƙari, ya kuma yi kira ga Gwamnatoci a kowanne mataki, da su tabbatar da an raba kayayyakin rage raɗaɗin cire tallafin Mai, a yadda ya dace.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button