Labarai

Masarautar Adamawa Ta Tuɓe Rawanin Hakimin Ribaɗu

Majalissar zartarwar Masarautar Adamawa, ta sauke Hakimin Ribaɗu, da ke yankin ƙaramar hukumar Fufore, Alhaji Giɗaɗo Abubakar, daga kan kujerar hakimcinsa.

Bayanin hakan, na ɗauke ne ta cikin wata wasiƙa da aka aikewa Hakimin, mai ɗauke da sa hannun Sakataren riƙo na Masarautar, Alhaji Kabiru Bakari.

“Majalissar zartarwar Masarautar Adamawa ta umarce ni da na rubuta maka wannan wasiƙa, domin sanar da kai amincewar Gwamnan jihar, na tunɓukeka daga muƙaminka.

“Ana umartarka daga miƙa dukkannin abubuwan Sarautar da ke hannunka, da su ka haɗarda katin shaida, ga Sakataren riƙon Masarautar Adamawa, da ke Yola, ba tare da ɓata lokaci ba”, a cewar wasiƙar.

Sai dai, har ya zuwa yanzu Masarautar bata bayyana tartibin dalilin sutale Rawanin Hakimin ba.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button