Masu Dalilin Aure Sun Gabatar Da Ƴan Mata 10 Ga Matashin Da Ya Mayar Da Miliyan 15, A Kano
Ƙungiyar masu Dalilin Aure ta jihar Kano, ta buƙaci Matashin nan da ke sana’ar tuƙin Adai-daita Sahu, Auwalu Salisu, da ya zaɓi ƴan mata huɗu daga cikin guda 10 da su ka gabatar masa, domin ya Aura.
Sunan matashi, Salisu, wanda ke gudanar da sana’ar tuƙin Adai-daita Sahu dai, ya karaɗe Shafukan Sada Zumunta, da ma kafafen yaɗa labarai, bayan da ya mayar da Naira miliyan 15 da wani ɗan kasuwar ƙasar Chadi, ya manta a cikin baburin Adai-daita sahunsa.
Tun bayan nuna wannan kyakykyawar ɗabi’a kuma, Salisun ya yi ta rabauta da tagomashi daga ɓangarori mabanbanta.
A ya yin da ita ma ta shiga Sahu, domin bawa Matashi Salisu mai shekaru 22 ta ta gudunmawar, ƙungiyar masu Dalilin Aure, ta bayyana cewar, akwai mata guda huɗu, waɗanda zai iya zaɓa ya Aura.
Shugaban ƙungiyar, Alhaji Mukhtar Inuwa Yakasai, shi ne ya miƙa wannan buƙata ga matashin, a ya yin zantawarsa da gidan Rediyon Freedom, da ke birnin Kano.
Shugaban ya ce, Babu shakka Matashin ya yi koyi da halin Ma’aiki Sallallahu Alaihi Wasallam, wanda hakan ya sa, ƙungiyar ke buƙatar karramashi, da kyautar Matan Aure.
Ya kuma ce, 2 daga cikin ƴan matan guda 10 ƴaƴansa ne.
“Matashin ya nuna kyakykyawan hali irin na Ma’aiki Sallallahu Alaihi Wasallam. Ya na buƙatar a karrama shi saboda gaskiyarsa. Hakan ne ya sa mu ka shirya karrama shi da waɗannan ƴan matan.
“Mata 10 ne, mu ke son ya zaɓi guda huɗu. Biyu daga cikinsu ma ƴaƴana ne”, a cewar Shugaban.