Tsaro

Masu Garkuwa Da Mutane Sun Buƙaci A Ƙara Musu Miliyan 200, Bayan Karɓar Miliyan 13 Tun Da Fari

Ƴan ta’addan da su ka yi garkuwa da masu hidimar ƙasa takwas, ƴan asalin jihar Akwa Ibom, a jihar Zamfara, sun buƙace a ƙara musu Naira miliyan 200 na kuɗaɗen fansa, bayan karɓar miliyan 13 da Iyalan waɗanda aka sace ɗin su ka bayar.

An sace masu hidimar ƙasar ne dai, tun a ranar 17 ga watan Augusta, a hanyarsu ta tafiya jihar Sokoto, domin halartar sansanin horas da masu yiwa ƙasa hidima.

Wani Ɗan Uwan guda daga cikin waɗanda lamarin ya rutsa da su, cikin yanayi na damuwa, ya bayyana wa Jaridar Vanguard cewar, masu garkuwar sun sake buƙatar ƙarin Naira miliyan 200 kafin sakin ƴan hidimar ƙasar guda bakwai, da Direban kamfanin zirga-zirgar Motocin Akwa Ibom (AKTC).

Ya na mai cewar, ” Bamu san inda za mu samo waɗannan maƙudan kuɗaɗen da su ka buƙata ba. Dukkanninmu mun yi mamakin hakan, domin kuwa Iyayen biyu daga cikin ƴan uwan namu da aka sace ne, su ka bayar da Naira miliyan 8 ɗin da aka basu a karo na biyu (su ka zama 13), bayan mun haɗa miliyan 5 mun basu a farko. Amma ya yin da mu ke dakon ganin masu garkuwar sun sake su kuma, sai kawai su ka tuntuɓemu su ka buƙaci mu ƙara musu miliyan 200, bayan Sha Ukun da mu ka biya tuntuni.

“Bamu samu wani taimako ba, daga ɓangaren Gwamnati. Mun sha wahala matuƙa kafin iya haɗa miliyan 13 ɗinma.

“To ta yaya zamu iya haɗa kuɗin fansar miliyan 200 ?. Muna cikin wani hali, kuma mun rasa taimako”.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Check Also
Close
Back to top button