Masu Jajayen Huluna Sun Mamaye Harabar Kotun Ɗaukaka Ƙarar Zaɓen Gwamnan Kano
Wasu rahotanni daga Kotun ɗaukaka ƙara, da ke babban birnin tarayya Abuja, da wakilin Rariya Online, Alhaji Sani Ahmad Zangina ya rawaito, sun bayyana yadda ƴan jam’iyyar NNPP ƙarƙashin ɗariƙar Kwankwasiyya, su ka mamaye harabar Kotun, sanye da jajayen huluna, inda su ke dakon hukuncin da Kotun za ta zartar kan shari’ar zaɓen Gwamnan jihar Kano.
Jam’iyyar NNPP da Ɗan Takararta na zaɓen Gwamna ne dai, su ka ɗaukaka ƙara, su na ƙalubalantar hukuncin da ƙaramar Kotun sauraron shari’ar zaɓen Gwamnan jihar ta zartar, tun a ranar 20 ga watan Satumba, wanda ya bayyana ɗan takarar APC, Nasiru Yusuf Gawuna, a matsayin sahihin wanda ya lashe zaɓen kujerar Gwamnan jihar, bayan da Kotun ta soke wasu ƙuri’u sama da 165,000 daga cikin ƙuri’un da ɗan takarar NNPP, kuma Gwamnan Kano a yanzu ya samu, bisa hujjar rashin sanya hannun jami’an hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC), da kuma Sitamfin hukumar.
Hukuncin Kotun ɗaukaka ƙarar kuma, na zuwa ne, kwanaki 10 bayan da Kotun ta kammala sauraron ƙarar da NNPP ɗin da ɗan takararta su ka ɗaukaka.