Masu Zanga-Zanga Sun Mamaye Majalissar Tarayya
Membobin ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa (NLC), da ke gudanar da zanga-zangar nuna adawa da tsadar rayuwar da ake cigaba da fuskanta a ƙasar nan, sun mamaye farfajiyar Majalissar Tarayya, da ke Abuja.
Masu zanga-zangar dai, na ɗauke da kwalaye ne, waɗanda ke nuna adawarsu kaitsaye ga halin matsin rayuwar da al’ummar ƙasar nan su ka tsinci kansu.
Zanga-Zangar ta kuma ɗauki harami a ɗaukacin biranen ƙasar nan, ciki kuwa har da Babban Birnin Tarayya Abuja, da birnin Lagos, har ma da Kanon Dabo.
Idan za a iya tunawa dai, kafin ɗaukar matakin tsunduma wannan zanga-zanga ta kwanaki biyu, NLC ɗin ta bada wa’adin makonni biyu ga Gwamnatin tarayya da ta aiwatar da yarjejeniyoyin da su ka cimma, tun a ranar 2 ga watan Oktoban shekarar da ta gabata, amma hakan ya ci tura.
Abin jira a gani kuma, bai wuce ko zanga-zangar za ta sanya Gwamnatin cika waɗancan yarjejeniyoyi ba, ko kuma akasin hakan.