Zamantakewa

Matar Da Ta Hallaka Ɗan Kishiyarta, Ta Samu Mazaunin Din-Din-Din A Gidan Gyaran Hali

Babbar Kotun jihar Kano, da ke Miller Road, a unguwar Bompai, ƙarƙashin Jagorancin Mai Shari’a Halima Sulaiman, ta yankewa wata mata mai suna, Rukayya Abubakar hukuncin ɗaurin rai da rai a gidan gyaran hali, bayan samunta dumu-dumu da laifin hallaka ɗan mijinta.

Lauya mai gabatar da ƙara, Barista Rabia Saad, ta bayyanawa Kotun cewar, Rukayyan ta jefa ɗan kishiyartata a rijiya ne, tun a shekarar 2021, wanda hakan ya yi sanadiyyar rasa ransa.

Barista Rabia ɗin, ta kuma ce laifin da Matar ta aikata, ya saɓa da tanadin sashe na 221 na kundin Penal Code.

A ya yin gudanar da shari’ar kuma, masu gabatar da ƙara sun gabatar da shaidun gani da ido guda huɗu.

A gefe guda kuma, an sake gurfanar da wata Matar mai suna, Shamsiyya Ashiru Gabasawa, bisa zarginta ita ma da kashe nata ɗan kishiyar.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button